Najeriya

Babu duriyar ma’aiktan man fetur tara da aka sace a Bayelsa

Wasu tsegerun Niger Delta da ake zargi da kai hare hare kan kamfanoni masu hakar mai a yankin Niger Delta
Wasu tsegerun Niger Delta da ake zargi da kai hare hare kan kamfanoni masu hakar mai a yankin Niger Delta AFP/PIUS UTOMI EKPEI

Wasu ‘Yan bindiga a Bayelsa, sun kama ma’aikatan wani kamfanin man fetur guda 9, tun ranar Alhamis, kuma ya zuwa yanzu ba’a san inda suke ba.

Talla

Rahotanni sun ce, ana kyautata zaton wadanda suka kashe ‘Yan Sanda 13 suka sace ma’aikatan, sakamakon munanan hare haren da dakarun dake aikin samar da tsaro a Niger Delta suka kaddamar a Yankin.

Kama ma’aikatan kamfanoni dake hakar mai a yankin an Niger Delta ba wani sabon abu bane inda zai yi wuya a kwashe mako guda ba tare da an sace wani ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI