Hukumomin kasar Masar za su samar da sabuwar doka kan kungiyoyi masu zaman kansu
Shugaban kasar Masar Mohammad Morsi, ya gabatar wa majalisar dokokin kasar wani daftarin doka, da zai kawo sauyi dangane da yadda kungiyoyi masu zaman kasansu ke tafiyar da ayyunkansu a kasar. Kamar dai yadda kungiyoyin kare hakkokin bil’adama na kasar ke cewa, matukar aka tabbatar da wannan doka, to zai kasance abu mai wuya su iya gudanar da ayyukansu a cikin ‘yanci.To sai dai gwamnatin ta shugaba Morsi wadda ta samu nasarar darewa kan karagar mulki bayan faduwar gwamnatin Husni Mubarak, ta ce a karkashin dokokin kasar da ake amfani da su a halin yanzu, gwamnati ba ta da masaniya kan yadda kungiyoyin ke samun kudade daga ketare balantana ma yadda suke kashe su.Ko a shekarar bara sai dai hukumomin kasar suka kame wasu masu gudanar da kungiyoyi masu zaman kan su.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: