Mali

Sabuwar kungiyar ‘Yan tawayen Mali za ta halarci taron samar da zaman lafiya

Wasu dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Mali
Wasu dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Mali Reuters

Wata sabuwar kungiyar ‘Yan tawayen Larabawan a kasar kasar Mali, ta ce za ta halarci tattaunawar samar da zaman lafiya da ake shirin gudanarwa a cikin watan Yuli mai zuwa tsakanin gwamnatin kasar da kuma sauran kungiyoyin ‘yan tawaye a karkashin jagorancin shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore.

Talla

Kungiyar mai suna MAA, ta gana da manzon na musamman da gwamnatin Mali ta tura zuwa birnin Nouackshot na kasar Mauritaniya, Tiebile Drame a marecen jiya Alhamis, 

Haka kuma kungiyar ta bayar da tabbacin cewa za ta shiga tattaunawa da za a buda a ranar 28 ga watan Yuli, wato a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugabancin kasar.

A daya bangare kuwa kasar Sweden, ta yi alkawarin aikewa da dakarunta 70 domin shiga rundunar wanzar da zaman lafiya da ke aiki a kasar ta Mali,
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.