Faransa-Africa

Faransa ta yi alkawarin taimaka wa nahiyar Afrika

Shugaba François Hollande, yayin hira da kafafen yada labarun Faransa
Shugaba François Hollande, yayin hira da kafafen yada labarun Faransa

Shugaban kasar Faransa Fracois Holland ya bayyana shirin kasar Faransa na taimakawa Nahiyar Afruka, don ta fita daga halin rashin tsaron da take fama da shi.Kasar ta Faransa, ta bayyana cewar ba zata dauki matakin Soji a kasar Libya, ba tareda goyon bayan Majalisar dinkin Duniya ba.Sai dai Faransa tace zata yi aiki da kasar ta Libya, domin kakkabe ‘yan tawaye a kasar.Shugaba Hollande ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga kafaifan watsa labarai na France24 da Gidan Radiyon Faransa da kuma TV5 MONDE a ranar juma’a.