Libya

Kotun duniya ta yi watsi da bukatar kasar libya kan dan Gaddafi

Dan marigayi Ghaddafi, Seif al - Islam
Dan marigayi Ghaddafi, Seif al - Islam 4.bp.blogspot.com

Kotun duniya ta yi watsi da bukatar gwamnatin kasar Libiya na neman da karta tuhumi Seif al Islam Khaddafi, dan tsohon shugaban kasar Marigayi Mouamar Gaddafi, matakin da aka jima ana jira. Wannan na matsayi na baya bayan nan, a ja’injar dake tsakanin kotun da kasar ta Libiya, kan wanda ya fi cancanta ya yiwa Seiful Islam shara’a.Wannan mataki da kotun ta duniya ta dauka, za’a iya cewa ya kawo karshen doguwar ja-in-jar shara’a, da ake yi tsakanin bangarorin biyu, sai dai kuma ba yana nufin kawo karshen nuna turjiyar da mahukumtan kasar ta libiya ke nuna wa ba kenan.