nijar

An kai hari rana ta biyu jere a juna a birnin Yamai na kasar Nijar.

Tarkacen motar da aka kai hari da ita a barikin sojan Agadez
Tarkacen motar da aka kai hari da ita a barikin sojan Agadez RFI / Sonia Rolley

Kwana daya bayan harin da aka kai wa gidan yarin birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro akalla biyu da kuma wasu daga cikin maharan, rahotanni daga birnin na Yamai, sun ce ko a tsakiyar ranar yau an yi wata arangama tsakanin jami’an tsaro da kuma wasu mahara a unguwar Poudriere da ke birnin, inda aka kashe akalla biyu daga cikin maharan.

Talla

Kawo yanzu dai ba wasu cikakkun bayanai daga bangaren hukumomin kasar dangane da fauwar wannan lamari na yau, yayin da hankulan jama’ar birnin na Yamai suka yi matukar tashi sakamakon faruwar wannan lamari.

To sai dai kamar yadda wadanda suka shaidi lamarin ke cewa, akwai yiwuwar wadanda jami’an tsaron suka kashe mazauna unguwar ne amma ba mahara ba.

A ranar asabar da ta gabata, an dauki dagon lokaci ana jin karar harbe-harbe a cikin gidan yarin birnin Yamai, fadar gwamantin kasar.
Shaidu a birnin na Yamai sun ce an soma jin karar harbe harben ne da misalin karfe uku na ranar yau, kuma bisa ga dukkan alamu wasu fursunoni ne suka karbe makamai daga hannun jami’an tsaron gidan yarin, wanda ke tsakiyar birnin na Yamai, inda suka afka wa jami’an dake gadin gidan.
Kawo yanzu dai, ba wasu cikakkun bayanai a game da hakikannin wadanda suka kai wannan hari, yayin da aka tura dimbin jami’an tsaro domin yi wa gidan yarin kawanya.
Wannan lamari dai yana faruwa ne mako daya bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake, suka kai hare-hare a wani barikin soja da ke garin Agadez da kuma cibiyar kamfanin hako makamashin Uranium na Areva, mallakin kasashen Faransa da kuma Nijar a garin Arlit da ke Arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 30 cikinsu kuwa har da sojoji akalla 20.
Ministan Shari'a, kuma kakakin gwamnatin ta Niger, Maru Amadu ya tabbatar da harin, inda ya ce wasu daga waje ne suka kai.
ministan ya kuma tattabatar da mutuwar akalla mutane 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI