Masar

Kotun kolin kasar Masar to soke Majalisar Dattawan kasar.

Masu adawa da gwamnatin Masar
Masu adawa da gwamnatin Masar REUTERS/Stringer

Madaukakiyar kotun kasar Masar a yau lahadi ta yi watsi da halascin Majalisar Dattawan kasar, wace za ta ci gaba da tafiyar da aiki har sai a gudanar da wani sabon zaben majalisar dokokin a kasar, kamar yadda fadar shugaban kasar Mohamed Morsi ta sanar.

Talla

Dama dai wannan hukumci na kotu ne, ake jira wajen kawo karshen ja-injar-da ake yi tsakanin bangaren gwamnati da ‘yan adawa, a kasar da ke cikin halin rudanin siyasa, tun bayan zanga zangar al’umma da ta kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.