Faransa-Libya-Mali

Faransa zata Taimakawa Libya da Mali koran 'Yan tawaye

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande rfi

Faransa ta yi alkawarin taimakawa kasar Libya da Mali domin  kawo karshen samame da kutse da 'yan tawaye ke kaiwa.Wannan tabbaci na zuwa ne daga bakin Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian inda yake nuni da cewa bisa dukkan alamu yankin sahara na neman zama mafakan ‘yan tawaye musamman masu tsananin kishin addinin Islama.Ya fadawa taron manema labarai a Singapore cewa akwai rahotannin jamian tsaro dake nuna cewa kudancin kasar Libya na da hatsarin gaske saboda a’lamarin ‘yan tawaye masu tsananin kishin Islama.Ministan ya nanata tabbacin da Shugaban Faransa Francois Hollan ya bayar, a tattaunawa dashi cewa Faransa ba zata tura Dakarun ta zuwa ba sai idan an sami amincewar Majalisar Dinkin Duniya.