Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

An kai harin a garin Bouca dake Afrika ta tsakiya

rfi

A kasar Jamhuriyar tsakiyar Afrika, an samu mutuwar mutane 7 a wani hari da rahotani suka ce ‘Yan tawayen Seleka ne suka kai a garin Bouca,akalla dai mutane da dama ne aka bayyana sun jikkata. Wata majiya tace mayakan sun shigo ne da sunan kare rayukan mutane amma daga bisani suka farma wa gidajen mazauna garin.‘Yan tawayen Seleka ne dai suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize a ranar 24 ga watan Maris inda yanzu daya daga cikin su Michel Djotodia ne a saman madafan ikon kasar.