Amirka-Nigeria-Mali-Algeria

Amirka ta Ware $23m Domin Kamo masu Rikicin Addini A Africa ta Yamma

Soja Nigeria dake farautar masu tsananin kishin Islama
Soja Nigeria dake farautar masu tsananin kishin Islama rfi

Kasar Amirka ta yi tayin  makudan kudade  Dolan Amirka Miliyan 23 domin a kamo mata Shugabannin kungiyoyi 5 na masu tsananin kishin Islama a yankin Africa ta Yamma.Tayin na  nuna cewa akwai  kyauta mafi tsoka na kudin Amirka Dola miliyan  akwai  za’a baiwa duk wanda ya kama Jagoran kungiyar Boko Haram a Nigeria ne  Abubakar Shekau, wanda wai a makon jiya ya nemi masu kishin Islama a kasashen Afghanistan, Pakistan da Iraki su shiga fafutukan kafa addini musulunci zalla a Nigeria.Shirin bada kyautan na Amirka ya yi tayin bada makudan kudade domin kamo Shugabannin Kungiyoyin addinin biyar  a yankin Africa ta yamma.An ware Dola miliyan biyar don baiwa  wanda ya kama Mokhtar Belmokhtar, malami mai ido daya da ake zargi da hannu wajen harin da aka kai wata ma’aikata a kasar Algeria a watan daya inda mutane 37 ‘yan kasashen waje suka mutu.An kuma ware Dolan Amirka miliyan 5 don baiwa duk wanda ya kama Yahya Abou Al-Hamman wanda ake zargi da hannu wajen kisan wani Bafaranshe da akayi garkuwa dashi a kasar NigerAmirkan ta kuma ware kudi Dollan Amirka miliyan 3 domin a kamo mata Malik Abou Abdelkarim, da Oumar Auld Hamada wanda shine kakakin kungiyar MUJAO.