Amirka-Nigeria-Mali-Algeria

Amurka ta ware Dala milyan 7 ga wanda ya taimaka don cafke Abubakar Shekau.

A tsakiya, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
A tsakiya, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau AFP PHOTO / YOUTUBE

Gwamnatin Amurka, ta yi alkawalin bayar da tukuicin Dala milyan 7, ga duk wanda ya taimaka ma ta da bayanan da za su kai ga cafke shugaban kungiyar Boko Haram a Najeriya wato Shek Abubakar Shekau.

Talla

A wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana ware dala milyan 23 a matsayin lada ga wadanda za su taimaka da bayanai domin cafke wasu da ta ce manyan ‘yan ta’adda ne a duniya, da suka hada da shugaban Boko Haram Shek Abubakar Shekau a kan dala milyan 7, sai shugaban kungiyar Alqa’ida a yankin Magreb Yahya Aboul Al-hamman dala milyan 5, sai wani jigo a kungiyar ta Alqa’ida a yankin Magreb mai suna Mokhtar Belmokhtar shi ma a kan dala milyan 5 a cewar sanarwar.

Har ila yau ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta ambaci wasu mutane biyu, Malik Abou Abdelkarim da kuma Oumar Ould Hamaha a matsayin manyan kwamandojin kungiyar Mujao da ke yaki a Yammacin Afirka, inda ta ware dala miliyan 3 ga duk wanda ya taimaka da labaran da su bayar da damar cafke kowanne daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI