Cote d'Ivoire

Kotun Kasa-da-Kasa na Bukatar Karin Hujjoji Game da Gbagbo

Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo
Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo rfi

Kotun kasa-da-kasa dake hukunta masu aikata manyan laifukan yaki ta  ce tana bukatar karin hujjoji da zasu sa a gurfanar da tsohon Shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, da ake zargi da laifukan yaki shekaru biyu da suka gabata.Wata sanarwa daga ofishin Kotun dake Hague na cewa alkalan kotun sun nemi masu shigar da kara dasu  gabatar da sabbin hujjoji ko kuma a ci gaba da bincike domin gurfanar da Laurent Gbagbo.A cewar Alkalan kotun hujjoji 45 da aka gabatar, zarge-zarge ne daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama.Alkalan sun bukaci a gabatar da shaidu ko hujjoji a zahiri da ke nuna tsohon Shugaban ko wani na hannun daman sa ya aikata laifi da ya kamata a gurfanar dashi.