Afrika ta Kudu

Oscar Pistorious Zai Sake shiga Kotu 19 Agusta

Oscar Pistorius
Oscar Pistorius rfi

Wata kotu a Pretoria na kasar Africa ta Kudu ta dage sauraron karar da aka shigar na fitaccen gurgu mai gudu da kafan karfe  Oscar Pistorious, wanda ake zargi da kashe budurwar sa Reeva Steenkamp.Kotu ta tsaida ranar 19 ga watan Agusta domin sauraron shariar.Dan shekaru 26 bayyanan sa ta farko kenan tun bayan bada shi beli da akayi.Wannan rana da aka tsaida zata kasance ranar da budurwar tasa za ta cika shekaru 30 da haihuwa.Kotu ta cika makil da ‘yan kallo a yau.