Mali

Sojan gwamnatin Mali na shirin kwato Kidal daga hannun 'yan tawaye.

Sojan Mali a cikin garin Kidal
Sojan Mali a cikin garin Kidal Reuters

Rahotanni daga kasar Mali, sun ce ayarin sojojin gwamnatin kasar na kan hanyarsu ta zuwa Kidal, yankin da yanzu haka ke karkashin ikon ‘yan tawayen kungiyar Azbinawa ta MNLA.

Talla

Kakakin sojan kasar ta Mali Suleman Maiga, ya ce sojojin sun tashi ne daga wani bariki da ke garin Gao, kuma za su ja daga ne a wani gari mai suna Anefis, daga can ne kuma za su kara daura damara domin shiga birnin na Kidal.
Wannan yunkuri da sojojin kasar ta Mali ke yi, ya zo ne a daidai lokacin da bayanai ke cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari a gidan shugaban kungiyar ta MNLA da ke garin na Kidal a yau talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.