Najeriya

Soji a Najeriya sun sanar da kara kama wasu ‘yan Boko haram 49

Sojan Najeriya a garin Baga na jihar Borno
Sojan Najeriya a garin Baga na jihar Borno REUTERS/Tim Cocks

Dakarun kasar Najerya masu fada da ‘ya’yan kungiyar Ahlussuha lidda’awati wal jihar ko Boko haram a yankin Arewa maso Gabashin kasar sun sanar da kama ‘ya’yan kungiyar 49. Sojin hakama sun bayyana cewar ‘ya’yan kungiyar na cigaba da barin Garuruwan su, suna fadawa wasu yankuna na Jamhuriray Nijar a dai dai lokacin da Sojin ke cigaba da fatattakar su.

Talla

Jihar Yobe na dai daga cikin jihohin da aka kakabawa Dokar ta-baci lokacin da aka yi fafatawa tsakanin Soji da Mayakan Boko haram Makwanni Ukku da suka gabata.

Mai magana da yawun Ma’aikatar tsaro ta kasar ya bayyana cewar an kama akalla ‘yan Boko haram 49 a fafatawar yau dinnan, a yayinda dukkanin sansanonin ‘ya’yan kungiyar suka kasance a yamutse sakamakon harin kwantam Baunan da Sojin suka kai a ranar Laraba.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta bayyana soke kungiyar ta Boko haram.

A karkashin wannan mataki, duk wanda aka sama yana alaka da kungiyar, na iya fuskantar daurin shekaru 20 a gidan yari.

Mai Magana da yawun shugaba Goodluck jonathan, Reuben Abati, ya ce matakin, ya kawo karshen halascin kungiyar, inda kuma ya yaba da sanarwar da kasar Amurka ta bayar dangane da tukuicin dala milyan 7 ga duk wanda zai taimaka da bayanan da za su bayar da damar kama shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI