Mali

An tsawaita wa'adin aiki da dokar ta baci a Mali.

Sojojin Chadi na aiki a kasar Mali
Sojojin Chadi na aiki a kasar Mali REUTERS/Adama Diarra

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugabancin kasar Mali a ranar 28 ga watan Yuli mai zuwa, hukumomi sun sanar da tsawaita wa’adin yin aiki da dokar ta baci a kasar.

Talla

Sanarwar bayan taro da ta fitar a yammacin jiya, majalisar ministocin kasar ta ce ta tsawaita wa’adin yin aiki da dokar har zuwa jajibirin buda yakin neman zabe wato ranar 5 ga watan Yuli.
Wannan mataki dai ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa ayarin sojojin gwamnatin kasar na kan hanyarsu ta zuwa Kidal, yankin da yanzu haka ke karkashin ikon ‘yan tawayen kungiyar Azbinawa ta MNLA.
Kakakin sojan kasar ta Mali Suleman Maiga, ya ce sojojin sun tashi ne daga wani bariki da ke garin Gao, kuma za su ja daga ne a wani gari mai suna Anefis, daga can ne kuma za su kara daura damara domin shiga birnin na Kidal.
Wannan yunkuri da sojojin kasar ta Mali ke yi, ya zo ne a daidai lokacin da bayanai ke cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari a gidan shugaban kungiyar ta MNLA da ke garin na Kidal a yau talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.