Habasha

Habasha ta yi biris da Masar, za ta ci gaba da gina madatsar ruwa a kogin Blue Nile

Firaministan Habasha, Hailmariam Desalegn
Firaministan Habasha, Hailmariam Desalegn REUTERS/Tiksa Negeri

Kasar Habasha ta ce za ta cigaba da gina madatsar ruwan kasar akan Kogin Blue Nile, matakin da Masar ta ce zai shafi samarwa kasar ruwan sha.

Talla

Getachew Reda, mai magana da yawun Firaminista, Hailemariam Desalegn, ya ce za su ci gaba da gina madatsar ba tare da la’akari da bukatar Masar ba.

Hukumomin Masar sun ce za su dauki matakan da suka dace, dan hana Habasha gina madatsar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.