Najeriya

Jami’an tsaron Najeriya sun cafke wanda ake zargi da kashe ‘yan sanda 11 a Niger Delta

Dakarun Najeriya
Dakarun Najeriya REUTERS/Eric Gaillard

Rundunar sojin Tarayyar Najeriya ta sanar da cafke wani mai suna Jackson Fabouwei, wanda ake zargin cewa shi ne ya shirya harin da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sandar kasar akalla 11 a yankin Niger Delta da ke kudancin kasar a cikin watan Afrilun da ya gabata.

Talla

Rahotanni sun ce jami’an tsaro da ke aiki karkashin rundunar hadin gwiwa ta JTF ne suka cafke Fabouwei a garin Yenagoa fadar gwamantin jihar Bayelsa a ranar 6 ga wannan wata na Yuni.

Binciken da jami’an tsaron suka gudanar na cewa, maharan sun kashe ‘yan sandan ne a kokarinsu na kashe daya daga cikin tsoffin kwamandojin kungiyar ‘yan gwagwarmayar yankin Niger Delta mai suna Kile Selky, wanda a halin yanzu ke rike da mukamin mai bai wa shugaban kasar Goodluck Jonathan shawara.

An kuma kai masa harin ne a lokacin da yake halartar jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu a cikin watan na Afrilu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI