Mali

Mali: Gwamnati da Azbinawa na tattaunawa a Burkina Faso

Dakaru na sinitiri a yankin Kidal dake hanun 'yan tawaye a Mali
Dakaru na sinitiri a yankin Kidal dake hanun 'yan tawaye a Mali Reuters

An yau ne za a soma tattaunawa gadan-gadan tsakanin Azbinawa ‘yan tawaye na kungiyar MNLA da kuma gwamnatin kasar Mali a karkashin jagorancin mai shiga tsakani na kungiyar kasashen yankin Yammacin Afirka ta CEDEAO/ECOWAS wato shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore.

Talla

Rahotanni daga birnin Ouagadougou inda wannan tattaunawa ke gudana, na nuni da cewa muhimman batutuwan da bangarorin za su fi mayar da hankali a kai sun hada da batun kwance damarar ‘yan tawaye na MNLA wadanda har yanzu ke rike da malamansu a yankin Kidal, kuma wannan batu ne zai mamaye tattaunawar har zuwa ranar litinin mai zuwa.

Ko baya ga shugaba Compaare da ke jagorantar tattaunawar, akwai wakilan gwamnatin Mali, da na ‘ya tawayen da kuma wadanda ke wakiltar kungiyoyin kasa da kasa da ke da hanu wajen warware wannan rikici na Mali.

Daya daga cikin manyan kalubalen da ke gaban mahalarta tattaunawar dai, shi ne batun gaggauta mai wa gwamnatin ta Mali damar aikewa da dakaru da kuma jami’anta a yankin Kidal da har yanzu ke hannun ‘yan tawaye da kuma sojojin ketare.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.