Africa ta Kudu

Ana gudanar da addu’o’in neman sauki ga Mandela

Tsohon shugaban kasar Africa ta Kudu, Nelson Mandela
Tsohon shugaban kasar Africa ta Kudu, Nelson Mandela Reuters

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, ya share tsawon dare na biyu kwance a wani asibitin birnin Pretoria sakamakon tsanantar matsalar huhu da yake fama da ita.

Talla

Likitan da ke kula da Mandela a wannan asibiti, ya ce matsalar da tsohon shugaban dan kimanin shekaru 95 a duniya ke fama da ita, ta kai wani matsayi na damuwa.

Rahotanni na nuna cewa ana ta gudanar da addu’o’i a sassa daban daban na kasar domin neman sauki ga tsohon shugaban a a mujami'u.

Daga watan disambar shekarar da ta gabata zuwa yau, wannan ne dai karo na hudu da ake kwantar da shi a asibiti sakamakon wannan matsala.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI