Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan ta dakatar da Sudan ta Kudu daga yin amfani da bututun manta

Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir
Shugaban kasar Sudan, Omar Albashir Reuters

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir ya bayar da umurnin dakatar da yin amfani fa bututun mai na kasar wajen fitar da danyan man fetur na Sudan ta kudu daga yau Lahadi, yana mai zargin makwabciyar kasar da ci gaba da taimaka wa ‘yan tawaye domin wargaza sha’anin tsaron kasarsa.

Talla

Har ila yau Al bashir ya bukaci matasa na kasar da su shiga aikin soja, sannan kuma su kasance a cikin shiri domin kaddamar da yakin kare kasar daga abokan hamayya.

Sai dai duk da cewa Albashir bai ambaci sunan wata kasa a matsayin abokiyar hamayya ba, wani na hannun damarsa ya ce Sudan ta kudu ce abokiyar hamayyar.

Matakin hanawa Sudan ta kudu yin amfani da manyan bututun domin isar da manta zuwa gabar teku, ya zo ne watanni uku bayan da kasashen suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.