Mali

UNESCO ta kai ziyara birnin Timbuktu

Ire iren wuraren da aka rusa a Timbuktu
Ire iren wuraren da aka rusa a Timbuktu

Tawagar kwarurru daga Hukumar Bunkasa Ililimi, kimiya da kuma Tattalin Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO, ta kai ziyara a birnin Tumbuktu domin ganema idanuwananta irin barnar da masu kishin Islama suka yi wa masallaci da kuma jami’ar musulunci da ke birnin bayan da suka kwace shi daga hannun sojojin gwamnatin Mali.

Talla

Rahotanni daga birnin na Tumbuktu na cewa akalla litattafai wadanda manyan malaman musulunci suka rubuta sannan kuma ake ajiye da su a cikin wannan jami’a guda dubu 4 ne suka bata daga lokacin da masu kishin Islamar suka shiga birnin, yayin da suka farfasa kaburburan mayan malamai akalla 16.

Hukumar ta Unesco dai ta ce a halin yanzu ana bukatar dalar Amurka miliyan 11 domin gudanar da ayyukan sake gina barnar da masu kishin Islamar suka yi wa jami’ar da kuma masallacin na Tumbukutu.

Wannan ziyara dai ta zo ne a daidai lokacin da aka shiga tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin gwamanatin Mali da kuma ‘yan tawaye a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI