Libya

Babban Hafsan sojin Libya ya yi murabus

Wani yanki da aka tafka rikici a Benghazi
Wani yanki da aka tafka rikici a Benghazi REUTERS/Esam Al-Fetori

Babban Hafsan sojin kasar Libya, Janar Yussef al-Mangoush, ya sauka daga mukamin sa, sakamakon mummunar harin da aka kai Benghazi, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 31, kana kuma sama da 100 suka samu raunuka.

Talla

Abdullahi al-Gmati, wakili a Majalisar mulkin kasar, ya ce dama suna shirin amincewa da kudirin dakatar da Janar din, kamin mika takardarsa ta murabus.

A yanzu haka gwamnatin rukon kwaryar kasar ta ba da hutun kwanaki uku domin yin jimamin wadanda suka rasa rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI