Faransa-Madagascar

Faransa ta bukaci ‘Yan takarar Madagascar guda uku su janye

Andry Rajoelina da Lalao Ravalomanana da Didier Ratsiraka, 'Yan takar Madagascar da Gwamnatin Faransa ta bukaci su janye
Andry Rajoelina da Lalao Ravalomanana da Didier Ratsiraka, 'Yan takar Madagascar da Gwamnatin Faransa ta bukaci su janye AFP/Montage RFI

Kasar Faransa ta bukaci uku daga cikin ‘Yan Takaran shugabancin kasar Madagascar su janye daga takarar zabe don kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar. ‘Yan takaran da ake bukatar janyewar su sun hada da shugaba mai ci Andry Rajoelina, da matar shugaban da aka kifar da Gwamnatin sa, Marc Ravolomanana da kuma tsohon shugaban kasa, Didier Ratsiraka.

Talla

Kakakin ma’aikatar wajen Faransa, Philippe Laliot, yace muddin wadannan mutane suka shiga zaben, Faransa ba za ta amince da sakamakonsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.