Afrika ta Kudu

Mandela ya kwashe kwanaki hudu a Asibiti

Wasu ayarin iyalin magidanci a Johannesburg, suna yi wa Nelson Mandela fatar samun samun sauki
Wasu ayarin iyalin magidanci a Johannesburg, suna yi wa Nelson Mandela fatar samun samun sauki REUTERS/Mujahid Safodien

Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu ya kwashe kwanaki hudu a gadon asibitin birnin Pretoria inda ya ke ci gaba da jinyar rashin lafiyar huhu da ya ke fama da ita. Dubban ‘Yan kasar Afrika ta kudu ne ke ci gaba da gudanar addu’oi domin ganin Mendela ya samu sauki.

Talla

Shugaba Jacob Zuma yace rashin lafiyar Dattijon ta yi tsanani amma yana nan yadda ya ke.

A ranar Assabar ne aka kwashi Mandela zuwa Asibiti, kuma kakakin gwamnatin Afrika ta Kudu Mac Maharaj, yace Likitoci na ci gaba da kula da lafiyar tsohon shugaban.

Likitoci sun ce Mandela ya dade yana fama da matsalar huhu, tun lokacin da ya kamu da matsalar tarin fuka a shekarar 1988.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.