Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu tana fatar sasantawa da Sudan cikin ruwan sanyi

Shugaban Kudancin  Sudan Salva Kiir a lokacin da ya gana da Shugaba Omar Hassan al-Bashir a birnin Juba
Shugaban Kudancin Sudan Salva Kiir a lokacin da ya gana da Shugaba Omar Hassan al-Bashir a birnin Juba Reuters

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir yace zai mika rikicin da kasar sa ke yi da Sudan ga kungiyar Tarayyar Africa domin warware sabanin amma ba su koma fagen yaki ba. A ranar Lahadi ne kasar Sudan ta jingine yarjeniyoyi 9 da suka kulla da sudan ta Kudu da suka shafi tsaro da tattalin arziki, ciki har da batun fitar da mai da kasar Sudan ta kudu ke yi, inda kasar Sudan ke fadin cewa zata mayar da zumuncin idan har kasar Sudan ta kudu ta dai na taimakawa ‘yan tawaye da ke uzurawa Sudan.

Talla

Tuni dai Sudan ta kudu ta musanta zargin tana taimakawa ‘Yan tawaye.

Barnabas Marial Benjamin ke cewa sharata kawai kasar Sudan ke yi cewa ana taimakawa ‘tan tawaye.

Kakakin gwamnatin Sudan ta Kudu Barnabas Marial Benjamin yace idan akwai abubuwan da yarjejeniyar ta nemi a yi idan har an yi zargin suna taimakawa ‘Yan tawaye.

Bangarorin biyu dai suna da ‘yancin shikar da kara karkashin yarjejeniyar da aka cim ma Kwamitin hadin guiwa don tabbatar da tsaron kasashen biyu.

Kodayake Mista Benjamin ya amsa cewa wasu ‘Yan tawaye kusan 300 bisa jagorancin wani kwamanda sun shiga yankin Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.