Duniya

kananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida

Wasu kananan yara
Wasu kananan yara rfi

KUNGIYAR Kwadago ta duniya, tace kananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida ko kuma masu hidima a kasashen duniya, wanda ake danganta shi da bauta.Kididigar da hukumar ta bayar yau, a ranar yaki da bautar ta Majalidsar Dinkin Duniya, tace cikin adadin, kashi 3 bisa 4 dag acikin su, Yan mata ne, kana kuma sama da miliyan 6 da rabi daga cikin yaran, shekarun su basu wuce 5 zuwa 14 ba.Kungiyar tace matsalar na da girma a duniya, sai dai kuma tafi kamari a kasashen Burkina Faso, Ghana, Cote d’Ivoire da Mali.Rahotan kungiyar ya kuma koka kan yadda ake tura kananan Yan mata daga Habasha zuwa Gabas ta tsakiya dan aikin bauta a gidaje.