Ra'ayin masu saurare game da ranar yaki da Bautar da yara kanana a Duniya

Sauti 20:00
Wani yaro dauke da kwandon ciyayayi
Wani yaro dauke da kwandon ciyayayi DR

Kungiyar Kwadago ta duniya (ILO), tace kananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida ko kuma masu hidima a kasashen duniya, wanda ake danganta shi da bauta. Kididigar da hukumar ta bayar, a ranar yaki da bautar da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya, tace cikin adadin, kashi uku bisa hudu daga cikinsu, ‘Yan mata ne. Kungiyar tace matsalar na da girma a duniya, sai dai kuma tafi kamari a kasashen Burkina Faso da Ghana da Cote d’Ivoire da Mali. Masu Sauraren RFI Hausa sun bayyana Ra'ayinsu.