Mali

Mali na Bukatar Zaman Lafiya Kafin Zabe

Dan takaran Shugaban ci a kasar Mali Soumaila Cisse tare da wakilinmu Abdoulaye Issa
Dan takaran Shugaban ci a kasar Mali Soumaila Cisse tare da wakilinmu Abdoulaye Issa RFI Hausa

Daya daga cikin ‘yan takara zaben Shugabancin kasar MaliSoumaila Cisse ya bayyana damuwar sa game da matsalar tsaro da zai iya durkusar da kasar.Soumaila Cisse na magana ne a tattaunawa da Abdoulaye Issa a birnin Cotounou na kasar Benin.Yana mai fatan ganin an yi zaben kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.Yace batun raba kasar Mali zai yi wuya saboda bukatun wasu mutan kasar.A cewar sa da jimawa suka ja hankulan hukumomin kasar, amma kuma suka ki yin komi.