Sudan-Sudan ta Kudu

An kai wa sansanin sojan MDD hari a yankin Kordufan na Sudan

Sojan Majalisar Dinkin Duniya a Sudan
Sojan Majalisar Dinkin Duniya a Sudan

Rahotanni daga Sudan sun ce wani hari da aka kai a kudancin Kordufan, ya tarwatsa sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojan Habasha tare da raunata wasu soji biyu.

Talla

Gwamnatin Khartoum dai na zargin Juba da taimakawa ‘Yan tawaye a kudancin Kordufan. Tun a cikin makon da ya gabata ne kasashen biyu masu makwabtaka da juna suna shiga tankiya, wanda hakan ke barazana ga makomar yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.