Zimbabwe

Taron Kungiyar SADC ta kasashen Kudancin Afirka a wannan asabar

Shigaba da Firayi ministan Zimbabwe, Robert Mugabe a hangu da Morgan Tsavangirai a dama
Shigaba da Firayi ministan Zimbabwe, Robert Mugabe a hangu da Morgan Tsavangirai a dama Reuters

Shugabannin Kasashen Kudancin Afirka a yau asabar ne suke gudanar da taro a kasar Mozambique domin tattauna rikicin siyasa da makomar kasar Zimbabwe bayan samun sabani tsakanin shugaba Robert Mugabe da kuma abokin hammayrsa Morgan Tsvangirai.

Talla

Zimbabwe dai na neman fadawa cikin rikici siyasa ne, bayan Morgan Tsvangirai ya yi wasti da ranar zaben da shugaba Mugabe ya bayyana.
Tsvangirai ya ce zai kalubalanci duk wata ranar zaben da Mugabe ya sa ba tare da sauya tsarin tafiyar da dimokuradiyyar kasar ba wanda zai tabbatar da kuri’un ‘yan kasar.
Shugabannin kasashen na Kuduncin Afrika za su yi kokarin warware rikicin tare da tattauna yadda zaben kasar zai kasance da kuma kafa gidauniya don tallafawa kasafin kudin zaben, yayin da rikicin siyasar Madagascar zai zama na biyu a wannan taro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI