Jamuriyar Afrika ta Tsakiya

‘Yan tawayen Afrika ta tsakiya sun hallaka mutane 16

Dakarun Afrika ta Kudu tare da suna sintiri tare da dakarun Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Dakarun Afrika ta Kudu tare da suna sintiri tare da dakarun Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Reuters/Luc Gnago

Wani hari da ‘yan tawayen kungiyar Lords Resistence Army na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya suka kai wasu kauyuka ya hallaka akalla mutane 16. 

Talla

Rahotanni sun ce, ‘yan tawayen sun kai harin ne a kauyukan dake Yankin Bria, inda suka kashe mutane shida, kana mutanen kauyan suka bisu inda suka kashe hudu daga cikin su.

Ganin anyi musu illa, sai ‘yan tawayen suka sake komawa inda suka kashe wasu mutane shida.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI