Najeriya

Kotu ta wanke Rashawa 8 da ake tuhuma da shigowa Najeriya da makamai

wasu jiragen ruwa na shawagi kan teku
wasu jiragen ruwa na shawagi kan teku REUTERS/China Daily

Wata kotu a birnin Lagos na tarayyar Najeriya, a yau talata ta wanke 8 daga cikin mutane 15 ‘yan asalin kasar Rasha, wadanda ake zargi da shigowa da makamai a cikin kasar, yayin da kotun za ta ci gaba da sauraran shari’ar sauran mutanen a cikin wannan mako.

Talla

Mutanen 15 wadanda dukkaninsu ma’aikatan wani kamfanin sufurin jiragen ruwa ne mai suna Myre Sea-diver, an cafke su ne a cikin watan oktoban shekarar da ta gabata a gabar ruwan Najeriya, inda kuma aka same su dauke da bindigogi.

Su dai hukumomin tsaron ruwan Najeriya, sun ce sun kama mutanen ne a daidai lokacin da suka shigo kan ruwan kasar da makaman da ba su sanar da hukumomin kasar cewa suna dauke da su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.