Libya

Kotun Libya ta wanke wasu jami’an Kanal Ghaddafi

Wani Dutse kusa da inda harin Lockerbie ya faru a yankin Scotland
Wani Dutse kusa da inda harin Lockerbie ya faru a yankin Scotland Reuters/David Moir

Wata Kotu a Libya, ta wanke wasu jami’an Tsohon shugaban kasa, Muammar Ghadafi guda biyu daga tuhumar da ake masu na hannu akan jirgin Lockerbie da ya halaka mutane 270. Lauyan da ke karar mutanen biyu, yace kotun ta wanke Abdelati al-Obeidi da Mohammed Belgasem al Zwai daga zargin, sai dai za a ci gaba da tsare su kan wani zargi na daban.