Mali

An kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawaye

Wakilan Azbinawa 'yan tawaye a tattaunawar sulhun birnin Ouagadougou
Wakilan Azbinawa 'yan tawaye a tattaunawar sulhun birnin Ouagadougou AFP/AHMED OUOBA

Gwamnatin Mali da kuma Azbinawa ‘yan tawaye, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu, bayan share tsawon kwanaki suna tattaunawa a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso.

Talla

A karkashin wannan yarjejeniya dai, bangarorin biyu sun amince ne da muhimman batutuwa da za su bayar da damar gudanar da zaben shugabancin kasar da ake shirin yi a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara.
Ministan harkokin mulki na kasar Mali ne Kanar Moussa Sinko Coulibaly ya sanya hannu amadadin gwamnatin kasarsa, yayin da Bilal Ag Acherif da kuma Algabass Ag Intalla suka sanya hannu a matsayin wakilan kungiyoyin ‘yan tawaye guda biyu a gaban shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore mai shiga tsakani a wannan tattaunawa.
To sai dai wasu daga cikin muhimman batutuwan da ke cikin wannan yarjejeniya sun hada da batun kwancewa ‘yan tawaye da ke mamaye da yankin Kidal damara, wanda kamar yadda yarjejeniyar ke cewa ba za a kwance damarar ba sai bayan an gudanar da zabe da kuma kafa gwamnatin dimokuradiyya, inda za a sake sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI