Mali

‘Yan sandan Mali sun cafke ‘Yan rajin kare hakkin bil’adama 21

Zauren tattaunawa tsakanin gwamnatin Mali da 'Yan tawayen Abzinawa a Ouagadougou kasar Burkina Faso.
Zauren tattaunawa tsakanin gwamnatin Mali da 'Yan tawayen Abzinawa a Ouagadougou kasar Burkina Faso. AFP/AHMED OUOBA

‘Yan Sanda a kasar Mali sun tsare wasu masu rajin kare hakkin Bil Adama 21, da ake zargi da shirya zanga zanga domin adawa da tattaunawar da Gwamnati ke yi da ‘Yan Tawayen kasar. ‘Yan rajin sun ce Gwamnati ta sassautawa ‘Yan Tawayen da dama.

Talla

Cikin wadanda aka kama, har da Mamatou Diabate, shugaban kungiyar kare hakkin Bil Adama ta FOSCM. Ya zuwa yanzu dai Mali na karkashin dokar ta baci ne, wanda ya hana gudanar da zanga zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.