Mali

Akwai kalubale a gaban Mali bayan sasantawa da ‘Yantawaye

Shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré, tare da Shugaban Mayakan Ansar Dine, Alghabass Ag a Ouagadougou.
Shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré, tare da Shugaban Mayakan Ansar Dine, Alghabass Ag a Ouagadougou. AHMED OUOBA / AFP

Babban kalubalen da ke gaban gwamnatin Mali shi ne na kokarin shirya zaben shugaban kasa cikin kwanaki 40 bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da ‘Yan tawayen Abzinawa. A ranar Talata ne gwamnatin Mali da ‘Yan tawaye suka sasanta bayan kwashe kwanaki 10 ana tattaunawa a Burkina Faso.

Talla

‘Yan tawayen sun amince Sojin kasar su shiga Kidal a yankin arewacin Mali domin samun kada kuri’a a zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga watan Juli.

Sai dai duk da ya ke bangarorin biyu sun amince da yarjejeniyar, amma masana suna ganin yana da wahala  a aiwatar da yarjejeniyar kafin a kada kuri’ar zabe.

Amma masana suna ganin tantance Mayakan Abzinawa da sauran mayakan da ke yaki a Arewacin Mali babban kalubale ne.

Cikin yarjejeniyar dai babu wani batu da aka cim ma game da ajiye makaman ‘Yan tawaye.

Gwamnatin Mali dai ta cim ma yarjejeniyar ne tsakaninta da Mayakan Abzinawa da ke yakin kafa sabuwar kasar AZAWAD amma akwai mayakan MUJAO da Ansar Dine da ke yakin kafa shari’ar Musulunci a Arewacin Mali.

A watan Maris ne Sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula ta Amadou Toumani Toure, amma wannan ne ya budewa ‘Yan tawayen kasar kofar karfe ikon arewaci. lamarin da ya sa Faransa ta kaddamar da yaki domin kakkabe ‘yan tawayen.

Wani batu da masana suke ganin zai iya kawo baraka, shi ne batun yiyuwar tsayawar ‘Yan tawaye takara musamman a kujerar Majalisa saboda ana iya janye sammacin cafke su akan aikata laifukan keta hakkin Bil’adama.

Babban kalubalaen da ke gaban Mali shi ne mayaka masu tsatstsauran ra’ayin Islama wadanda ke ci gaba da buya a arewacin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI