Nijeriya

Ba zan sauka ba daga mukamin na Shugaban PDP,a cewar Bamanga Tukur

Alhaji Bamanga Tukur,  shugaban Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya
Alhaji Bamanga Tukur, shugaban Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya rfi

SHUGABAN Jam’iyar PDP a Nigeria, Alh Bamanga Tukur, yace ba zai sauka daga mukamin sa ba, kamar yadda ake ta rade radi. Bayan ganawa da shugaban kasar, Goodluck Jonathan, Bamanga Tukur yace babu gaskiya a maganar.An samu rarrabuwar kawuna tsakanin manyan Yan Jam’iyar ta PDP kan Alh Adamu Mu’azu, tsohon Gwamnan Bauchi a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin Bamanga.Gwamnonin dake goyan bayan shugaba Jonathan ciki harda Gwamna Jihar sa, na da shakku kan baiwa Muazu kujerar.