Kenya-ICC

William Ruto zai kauracewa zaman kotun ICC

William Ruto a  lokacin  da  ya  bayyana  a  gaban kotun
William Ruto a lokacin da ya bayyana a gaban kotun rfi

KOTUN Hukunta manyan laifufuka dake birnin Haque, ta baiwa mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto, damar kauracewa zaman kotun, a tuhumar da ake masa, na hannu wajen kashe mutane 1,100 da akayi a shekarar 2007.Kotun tace ta amince da bukatar William Ruto saboda aikin da ke gaban sa, na ofishin mataimakin shugaban kasa.Da dama daga cikin yan siyasa a Nahiyar Afika suka yaba da wanan matakin  inda a gani sun wata nasara ce.Ya  zuwa  yanzu  hukumomin a  Kenya  ba su  bayar  da sanarwa  ba  kan wanan matakin  na  kotun  ICC.