Najeriya

‘Yan bindiga sun kashe mutane 48 a Zamfara

Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya
Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya

Wasu ‘Yan bindiga sun hallaka mutane kusan 50 a Kizara, da ke karamar hukumar Tsafe a arewa maso yammacin Najeriya. Bayanai sun ce, ‘Yan fashi ne suka je kauyen ne da asubahin Talata, inda suka abkawa mutanen garin, kuma cikin wadanda suka kashe akwai limamin garin da wani Basarake.

Talla

Jihar Zamfara na daga cikin Jiihohin da ‘Yan bindiga suka mayar dandalin kashe kashe, abinda ya ke jefa shakku kan rawar da jami’an tsaro ke takawa a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI