Kenya-ICC

An dage sauraren karar Kenyatta na Kenya har zuwa watan Nuwamba

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta Reuters

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague, ta bayyana 12 ga watan Nuwamban wannan shekarar, a matsayin ranar da za ta soma gudanar da shari’ar shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, wanda ake zargi da hannun wajen tayar rikicin da ya biyo bayan zaben shugabacin kasar na shekarar 2007. Wata sanarwa da kotun ta fitar ta tabbatar da dage sauraren karar, inda ta kara da cewa kotu ta yanke shawarar dage ranar soma gudanar da shari’ar shugaban kasar ta Kenya, zuwa ranar 12 ga watan nuwamba, a maimakon ranar 9 ga watan Yuli na zuwa.Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan wata doguwar tattaunawa, da aka yi tsakanin lawyoyin shugaban kasar da kuma bangaren masu gabatar da kara, wadanda suka bukaci karin lokaci domin kintsawa, don kare wanda ake tuhumar da aikata laifufuka daban daban har guda 5.Daga cikin wadannan zarge-zarge da ake yi wa Kenyatta mai shekaru 51 a duniya, har da kisan jama’a, cin zarafin dan adam, fyade da kuma tilasta wa jama’a barin gidajensu. Wadannan dai su ne jerin laifukan da ake tuhumar shugaban na Kenya sakamakon rikicin da ya barke bayan kammala zaben shugabancin kasar a shekara ta 2007, inda aka samu asarar rayukan mutane a kalla 1100, da kuma raunata wasu masu tarin yawa.