IMF-Masar

Masar na tattaunawa da IMF don karbar bashin kudi

Hukumar Lamani ta Duniya IMF, tace tattaunawar da take yi da hukumomin kasar Masar, kan bashin da kasar za ta karba, na samun ci gaba. Mai magana da yawun asusun na IMF, Gerry Rice ya ce aikin da suke yi da hukumomin kasar ta Masar na samar da karin fahimtar juna, kan muhimman batutuwa.Lokacin da yake magana a yayin wani taron manema labaru, Rice yace asusun na IMF na aiki kafada da kafada da hukumomin kasar ta Masar, don ganin an kammala duk wasu tsare tsaren da ake bukata, don kulla yarjejeniyar bayar da bashin.Ya ce batutuwan da za su duba, sun hada da yadda hukumomin kasar ta Masar za su rinka karbar haraji, don rage gibin kasafin kudin da ake samu, tare da janye tallafin da suke bayarwa kan farashin mai.Asusun na IMF ya shafe watanni yana tattaunawa da hukumomin kasar ta Masar, kan bashi biliyoyin Dalolin Amurka, lamarin da ya dogara kan goyon baya, daga masu ruwa da tsaki a fagen siyasa, da kuma sauye sauye a bangaren tattalin arzikin kasar, daga bangaren gwamnati. 

Shugaban Masar Mohamed Morsi
Shugaban Masar Mohamed Morsi AFP PHOTO/FAYEZ NURELDINE