Afrika ta Kudu

Motar daukar Mandela zuwa Asibiti ta samu matsala

Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu, Nelson Mandela
Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu, Nelson Mandela REUTERS/Michael Kooren

Motar da ake daukar Nelson Mandela zuwa Asibiti tsawon makwanni biyu ta samu matsala sai da aka nemi wata amma hakan be shafi lafiyar tsohon shugaban ba, kamar yadda kakakin gwamnatin Afrika ta kudu Mac Maharaj ya tabbatar.

Talla

An bayyana cewar motar ta samu matsalar Injini ne tana dauke da Mandela daga gidansa da ke Johannesburg zuwa asibitin da ake diba lafiyar shi a Pretoria.

Likitoci sun ce tsaikun da aka samu bai shafi lafiyar tsohon shugaban na Afrika ta kudu ba da ke ci gaba da jinya tun a ranar 8 ga watan Juni da aka sake kwantar da shi a Asibiti saboda matsalar huhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI