Masar

Dakarun Masar za su dauki mataki idan rikici ya barke - Minista

Masu adawa da gwamnatin Shugaba Muhammed Morsi
Masu adawa da gwamnatin Shugaba Muhammed Morsi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Ministan tsaron kasar Masar, Abdel Fattah al Sisi, ya ce sojin kasar zasu dauki mataki muddin aka samu barkewar rikici tsakanin masu goyan bayan shugaba Mohammed Morsi da masu adawa da shi.

Talla

Ministan ya ce, dokar kasa ta baiwa sojin damar sanya hannu dan hana kasar fadawa cikin tashin hankali, saboda haka ya zama masu wajibi su sanya hannu wajen magance duk wani rikicin da ya fi karfin ‘yan sanda.

Masu adawa da shugaba Morsi na zarginsa ne da juya ma mutanen kasar baya a lokacin da suka mara mai baya yah au karagar mulki bayan tintsirar da tsohowuar gwamnatin Hosno Mubarak.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI