Kenya

An hallaka mutane 10 a Kenya bayan harin gurneti

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta

Hukumomin kasar Kenya sun ce akalla mutane 10 aka kashe a wani harin gurnati da aka kai sansanin ‘yan gudun hijira, dake kusa da iyakar Somalia da Habasha.

Talla

Wani jami’in ‘yan sanda ya tabbatar da mutuwar mutanen, kusa da inda ake samun tashin hankali tsakanin kabilun Garre da Degodia.

Shugaban ‘yan sandan Kenya, David Kimaiyo, ya ce wasu mutane ne su biyu zuwa uku suka tare mutane suna kasshe bawai fadan kabilanci ban e.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI