Mukaddashin Gwamnan Taraba, Alh Garba Umar UTC

Sauti 04:14
Danbaba Suntai gwamnan Jahar Taraba da ke jinya a Amurka
Danbaba Suntai gwamnan Jahar Taraba da ke jinya a Amurka saharareporters

An samu rarrabuwar kawuna dangane da lafiyar Gwamnan Taraba a Najeriya Danbaba Suntai. Inda wasu ke cewa ya dace a yi amfani da kundin tsarin mulki don gudun kada Jihar ta fada cikin rudanin siyasa da zai hana aiwatar da ayyukan raya kasa, wasu na cewa ya dace a shafawa Gwamnan lafiya wanda ke ci gaba da jinya a Amurka. Mukaddashin Gwamnan, Alh Garba Umar UTC wanda ya kai mai ziyara ya shaida wa RFI halin da gwamnan ya ke ciki.