Ra'ayin masu saurare game da matsalar fashin jiragen ruwa a Afrika

Sauti 18:48
'Yan fashin jirgin ruwa a Somalia
'Yan fashin jirgin ruwa a Somalia Reuters/Feisal Omar

An bude taron kasashen da ke Yammaci da Tsakiyar Afrika a kasar Kamaru domin nazarin hanyar da za’a bi don magance matsalar da ake samu na fashin jiragen ruwa da kuma satar mai a tekun da ke Yankin Guinea. Rahotan hukumar da ke kula da sufurin jiragen ruwa, yace an samu karuwar fashin a mashigin ruwan Guinea, inda ya ribanya wanda aka samu. Masu sauraren RFi hausa sun bayyana ra’ayinsu tare da Nasirudden Muhammad.