Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan ta sake barazanar dakatar da tura mai zuwa Sudan ta Kudu

Shugaban kasar Sudan Omar al-bashir
Shugaban kasar Sudan Omar al-bashir Reuters

Shugaban kasar Sudan, Umar Hassan al Bashir, ya sake yin barazanar dakatar tura mai zuwa Sudan ta kudu, muddin makwabciyar ta ta bata daina taimakawa Yan Tawayen kasar ba.

Talla

Shugaba al Bashir ya ce, Sudan ta kudu taki aiwatar da yarjeniyoyi 10 da suka sanyawa hannu, banda na samar da mai, inda ya ke cewa muddin bata aiwatar da sauran ba, to zai hana turawa kasar mai.

Wanna kuma na faruwa ne a dai dai lokacin da wasu ‘yan kasar Sudan su 12 suka rasa rayukansu bayan wani bango ya rufta musu a ka a lokacin da suke jira su mika paspo dinsu na zuwa hajjin bana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.