Sudan

Fada tsakanin kabilu biyu ya yi sandiyyar asarar rayuka a Sudan.

Sakamakon wani fada da ya barke tsakanin kabilu biyu a yankin Darfur da ke kasar Sudan, akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a cewar majiyar tsaro da ke yankin.

Yankin Darfur a cikin jan launi.
Yankin Darfur a cikin jan launi. Map: de: Stern
Talla

Rahotanni sun yi nuni da cewa, fadan ya barke ne tsakanin kabilar Gimir da kuma Bani-Halba, wadanda a tsawon shekaru ba sa ga maciji na junansu, kuma tun a cikin watan Afrilun da ya gabata ne suke ci gaba da kai wa junansu hare-hare tare da haddasa asarar rayukan jama’a da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI