Mali

Masu shiga tsakanin rikicin Mali sun nemi akai zuciya nesa

Babban mai shiga tsakanin bangarorin Mali Tiebile Drame a zauren taron sasantawa à Ouagadougou
Babban mai shiga tsakanin bangarorin Mali Tiebile Drame a zauren taron sasantawa à Ouagadougou AFP/AHMED OUOBA

Babban Mai shiga tsakani a tattaunawar da aka yi tsakanin jami’an Gwamnatin Mali da 'Yan Tawayen kasar Tiebile Drame, ya bukaci al’ummar Mali su kai zuciya nesa kan yarjejeniyar da suka kulla. Kiran na sa ya biyo bayan sukar da ake wa sharuddun yarjejeniyar, inda ake zargin cewar Gwamnati ta sassautawa ‘Yan Tawayen da dama.

Talla

Jami’in yace ya ji kalamai da dama, amma ya dace a bai wa yarjejeniyar dama dan samun gudanar da zabe a kasar.

Yanzu haka, Rahotanni sun ce Sojojin Kasar Benin sun isa garin Kidal da ke Arewacin Mali, a karkashin yarjejeniyar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin duniya, kamar yadda ‘Yan Tawaye suka amince tsakaninsu da hukumomin Mali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI